An daga ziyara Saddam Hussai zuwa ranar laraba | Labarai | DW | 05.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An daga ziyara Saddam Hussai zuwa ranar laraba

A kasar Iraki, yau ne kotu ta koma shari´ar tsofan shugaban kasa Saddam Hussain, bayan an dage ta, a satin da ya wuce.

Da farko fara shariá r lauyoyin tsofan shuagaban kadar da su ka hada da tsofan ministan shari´a na kasar Amurika sun fita daga dakin shari´ar su ka kuma bayan da kotu ta biya bukatocin su.

A yayin da ya ke kare kan sa, daga zargin a ka yi masa na kashe mutane 148 a garin Dujail ,a shekara ta 1982,Saddam Husain yayi watsi da dukan zargin, tare da cewar wata makarkashiyar juyin mulki ce mutanen garin su ka bukaci shirya masa, kuma duk shugaban kasar da a ka yi wa yunkurin juyin mulki, ya zama wajibi a kan sa ya dauki mattakan hukunta wanda ke da alhakin abin makircin inji Saddam Hussain.

A yayin da mai shari´ar ya bukaci dakatar da Saddam lokacin da ya ke bayyani, tsofan shugaban ,ya maida masa martani da kakkausar halshe, cewar shi fa, ba shi tsoran hukuncin kissa, a game da haka, a bar shi ya barje gumen sa, dalla dalla a game da abubuwan da ya sani cikin wannan haraka.

Bayan sa ín sar, da a ka yi tsakanin alkalan da Saddam Hussain an dage shari`ar har ranar laraba mai zuwa.