An cimma yarjeniyoyi da yawa tsakanin China da Afirka Ta Kudu | Labarai | DW | 07.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cimma yarjeniyoyi da yawa tsakanin China da Afirka Ta Kudu

Shugaban China Hu Jintao ya yiwa ATK alkawarin zuba jari mai yawan gaske tare da fadada dangantakar tattalin arziki da siyasa tsakanin kasashen biyu. A ziyarar da ya kaiwa birnin Pretoria an sanya hannu kan yarjeniyoyi da yawa musamman a bangarorin makamashi da aikin noma. Shugaban ATK Thabo Mbeki ya ce ya zama wajibi nan gaba kasar sa ta daidaita huldododin cinikaiya tsakanin ta da China. Da farko ma´aikatar harkokin wajen China ta yi watsi da zargin da ake yi mata cewa tana bin manufofi na mulkin mallaka kuma ta fi nuna sha´awa ga cin gajiyar danyun kayan Afirka da take matukar bukata. Kungiyoyin kodago na ATK sun yi zargin cewa kayan tufafi da na lantarki masu araha daga China na kashe kasuwar wadanda ake samarwa a cikin gida.