1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An cimma yarjejeniyar zaman lahia tsakanin Tchad da Sudan

Shugabanin kasashen Tchad da Sudan ,sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lahia, a sakamakon taron Tripoli.

default

A daren jiya ne, bisa gayyatar shugaba Muhhamar Kaddafi na Lybia, a ka kammala taron sulhunta kasashen Tchadi da Sudan, da ke gaba da juna.

Wannan taro,ya samu halartar shugabanin kasashe 6 na Afrika, da su ka hada da Denis Sassun Nguesso na Congo ,wanda a halin yanzu, ke rike da matsayin shugaban tarayya Afrika, da Francois Bouzize, na Jamhuriya Afrika ta tsakiya, da Blaize Campaore na Burkina Faso, da shugaban kasar Sudan Omar Hassan El Beshir, da na Tchadi Idriss Deby, sai kuma mai masaukin baki Muhhamar Kadafi.

A tsawan yini guda, shugabanin sun tantana batutuwan da su ka gurbata huldodi tsakainTchadi da Sudan, tare da samar da hanyoyin magance su.

Idan ba a manta ba a watan desembner da ya wuce gwmanatin kasar Tchadi ta bayaan cewar ta shiga halin yaki da Sudan bayan ta same da hannu a kunna wutar tawaye.

A sakamakon wannan taro, Shugaba Idriss Deby, da takwaran sa, na Sudan Omar Hassan El Beshir, sun rataba hannu akan yarjeneiyar sulhu a tsakin kasashen 2, da har jiya basu ga maciji da juna.

Wannan yarjejeniya, ta tanadi sake kulla huldodin diplomatia da su ka katse tsakanin Tchadi da Sudan.

Kazalika kasashen 2, sun amince su dauki mattakan daina yi wa junan su, zangwan kasa, ta hanyar hadasa rikicin tawaye.

Sannan yarjejeniyar ta bukaci girka rundunar shiga tsakani, da kuma komitin da zai kunshi kassashen Afrika, bisa jagoranci Lybia, wanda za a dorawa yaunin bi, sau da kaffa ayyukan tabatar da wannan yarjejeniya a zahiri.

A yayin da suke jawabai, shugabanin kasashen 2, sun alkawarta mutunta wannan yarjejniya.

A jawabin sa, na rufe taro shugaba Kaddafi, ya kara jaddada wajibcin zaman lahia, tsakanin Tchad da Sudan, ya kuma yi kira ga yan tawayen kasashen 2, da su ajje makamai, su kuma tebrin shawara, domin abinda tantanawa cikin rowan sanhi bat a bada ba, ya na matukar wuya a same shi, ta hanyar yaki a nahiyar mu ta Afrika.

Shugaba Kaddafi, ya bada shawara rufe iyaka tsakanin Sudan da Tchadi, ta tsawan wani dan lokaci don hana kwararar yan tawaye, don cimma wannan buri Lybia a shire ta ke, ta bada gudummuwar mutane dubu 100, da motocin yaki 1000, da jirage 100.

Muhamar Kadhafi, ya kudurci hakan, saboda cimma burin sa, na ganin Afrika ta shawo kan matsala, ba tare da katsa landan ba, daga wasu kasashe na ketare, da su ka shahara, a shiga sharo ba shanu, cikin harakokin da su ka shafi Afrika.

Ya ce basu bukatar rundunar shiga tsakani ta Majalisar Dinkin Dunia, balle kuma dakararun Pramista Tony Blair.

Muhhamar Kaddafi, yayi wannan huruci, don maida martani ga ministan harakokin wajen Britania Jack Straw, da a makon da ya gabata, ya yi wa kasar Sudan, tayin kai dakarun shiga tsakani, na Majalisar Dinkin a yankin Darfur.

Shugaban kasar Lybia da ya jagoranci taron sulhun, ya yi kira ga shugaban hukumar zartaswa na kungiyar taraya Afrika Alfa Umar Konare, da ya dauki mattakan karfafa tawagar dakarun kwatar da tarzoma, da kungiyar taraya Afrika ta tura a yanki Darfur.

A shekara ta 2004, kungiyar ta tura dakaru dubu 7, a wannan yanki da ke fama da yakin bassasa, to saidai wannan runduna na fama da karancin kayan aiki.

 • Kwanan wata 09.02.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu1o
 • Kwanan wata 09.02.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu1o