An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Fatah | Labarai | DW | 30.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Fatah

An ci-gaba da arangama tsakanin kungiyoyin Falasdinawa da ba sa ga maciji da juna wato Hamas da Fatah a Zirin Gaza, duk da wata yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki cikin dare jiya. An amince da shirin tsagaita wutar ne bayan tattaunawar da aka yi tsakanin FM Falasdinawa Isma´il Haniyah da wani babban na hannun damar shugaba Mahmud Abbas na kungiyar Fatah. Dukkan sassan biyu sun amince su janye dakarunsu daga kan titunan Gaza. To sai duk da sanarwar tsagaita wutar an ji karar amon bindiga da fashewar wasu abubuwa a birnin Gaza. Da farko KTT ta yi kira ga sassan biyu da su kawo karshen tashe tashen hankula wadanda suka yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 30. Wata sanarwa da Jamus mai rike da shugabancin kungiyar EU ta bayar, ta nuna goyon baya ga shugaba Abbas da kuma kokarin sa na samun hadin kan kasa.