1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin Tchad da Sudan

February 9, 2006
https://p.dw.com/p/Bv8o

A sakamakon taron da ya gudana jiya a kasar Lybia, bisa gayyatar shugaba Kaddafi, kasashen Tchadi da Sudan, sun rattaba hannu, a kan yarjejeniyar sulhu tsakaninsu.

Shugaba Omar Hassan El beshir na Sudan da Idrissd Deby na Tchadi sun aminbce sun maida huldodin depolamtia,da su katse a tsakani su, kazalika yarjejeniyar da su ka rattaba hannu a kai, ta tanadi gwamnatocin kasashe 2, su hanna yan tawaye anfani da wasu daga yankunan kasashen su, domin kai hare haren tawayen ya zuwa daya daga cikin su.

Bugu da kari wannan yarjejeniya ta kudurci girka rundunar shiga tsakani da kuma wani komitin da kasar Lybia za ta jagoranta , wanda zai bi sau da kafa, wannan yarjejeniya.

Taron na kasar Lybia ya samu halartar shugabanin kasashen 6 da su ka hada da Dennis Sasun Ngesso na Congo, wanda a yanzu ke rike da matsayin shugaban taraya Afrika da Francois Buzize na Jamhuriya Afrkia ta tsakiya da Blaize Kampaore na Burkina Faso.