An cimma yarjejeniyar sulhu a tsakanin Fatah da Hamas | Labarai | DW | 02.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cimma yarjejeniyar sulhu a tsakanin Fatah da Hamas

Bangarorin dake rikici da juna a yankin Palasdinawa, sun amince da tsagaita bude wuta a tsakanin su.

Ya zuwa yanzu dai babu wani ingantaccen bayani dangane da abubuwan da yarjejeniya ta kunsa.

Wannan sabuwar yarjejeniya dai tazo ne bayan wata arangama da aka gwabza, a tsakanin magoya bayan jam´iyyar Fatah da kuma ta Hamas, wanda hakan yayi ajalin mutane 10.

Kafafen yada labarai sun rawaito shugaba Mahmud Abbas na kiran bangarorin biyu, dasu kawo karshen wannan rikici.

Tuni dai ofishin Faraministan, ya bayar da sanarwar cewa, Mahmud Abbas a wani lokaci an shirya zai gana da shugaban kungiyyar Hamas, wato Khaled Mashaal dake gudun hijira.

A na dai sa ran shugabannin biyu, zasu tattauna ne a game da batu na kafa gwamnatin hadin kai a yankin na Palasdinawa, domin kawo karshen rikicin dake tsakanin bangarorin biyu.