1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cimma yarjejeniyar hada gwamnatin Hadaka a Jamus

Mahukuntan jamiyyar SPD mai mulkin tarayyar Jamus ta zabi Mr Mathias Platzeck a matsayin sabon Shugabanta.

Mr Platzeck , wanda ya fito daga gabashin Jamus ya samu amincewar masu gudanar da wannan zabe da kuria a kalla kashi 99 da digo hudu, a lokacin wani taron kolin jamiyyar da aka gudanar a birnin Karlruhe.

Jamiyyar ta SPD ta zartar da hakan ne kuwa jim kadan bayan sun cimma yarjejeniya da jamiyyar adawa ta CDU da CSU, game da kafa gwamnatin Hadaka a tsakanin su.

Bayanai dai sun shaidar da cewa jim kadan bayan zabar sa a wannan sabon mukami, Mr Platzech yayi alkawarin daukar matakan gaggawa na dawowa da jamiyyar kimar ta, ta bangaren tafiya tare domin a tsira tare.

Wannan zabe na Mr Platzech dai ya biyo bayan, murabus din shugaban jamiyyar ne wato Mr Franz Muntefering. Duk dai da saukar tasa daga wannan mukami, ana sa ran Munteferin zai karbi mukamin ministan kwadago , kuma mataimakin shugabar gwamnati a cikin wannan gwamnati ta hadaka da za a kafa nan bada dadewa ba.

A dai mako mai zuwea ne ake sa ran majalisar dokoki ta Bundestag zata amince da zabar Angela Markel a hukumance a matsayin sabuwar shugabar gwamnatin Jamu