An cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin Mali da ´yan tawaye | Labarai | DW | 30.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin Mali da ´yan tawaye

Gwamnatin Mali da ´yan tawayen buzaye sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya bisa shiga tsakanin kasar Aljeriya. Wani mai shiga tsakanin na Aljeriya ya fadawa kamfanin dillanci labarun AFP cewa dukkan sassan biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar samar da zaman lafiyar. An cimma haka ne kuwa bayan da ´yan tawayen suka janye bukatar su ta nemawa yankin su ´yancin cin gashin kai. Ita kuma a nata bangaren gwamnatin Mali ta yi alkawarin daukar sahihan matakan raya yankin na Buzaye.