An cimma yarjejeniya tsakanin gwamnati da ´yan tawayen Nepal | Labarai | DW | 16.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cimma yarjejeniya tsakanin gwamnati da ´yan tawayen Nepal

Shekaru 10 bayan da kungiyar ´yan tawaye masu ra´ayin Mawo suka fara bore a Nepal, an cimma wata yarjejeniya tsakanin gwamnati da ´yan tawayen. Bayan wata ganawa da suka yi a birnin Kathamandu FM Girija Prasad Koirala da madugun ´yan tawaye Prachanda sun sanar da kafa wata gwamnatin riko wadda zata kunshi wakilan ´yan tawaye. Wannan gwamnati ce za´a dinkawa alhakin fasalta sabon daftarin kundin tsarin mulkin kasar. Ana ganin wannan sanarwa tamkar wata nasara ga masu ra´ayin Mawo wadanda suka dade suna neman a sake fasalta kundin tsarin mulkin. A karshen watan afrilu kawancen jam´iyu 7 karkashin FM Koirala suka tilastawa sarki Gyanendra maido da majalisar dokoki kana kuma suka tube shi daga mukamin sa. Bayan wannan lokaci gwamnati ta fara tattaunawa da ´yan tawaye.