An cimma yarjejeniya kan kasafin kudin kungiyar EU har zuwa shekara ta 2013 | Labarai | DW | 17.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cimma yarjejeniya kan kasafin kudin kungiyar EU har zuwa shekara ta 2013

Bayan tattaunawa mai tsawo, shugabannin KTT da ke taron koli a birnin Brussels sun amince da wani kasafin kudi ga kungiyar mai membobi 25. An cimma yarjejeniyar ce da sanyin safiyar yau asabar bayan da Birtaniya ta amince ta rage rangwamin da ake mata da kimanin Euro miliyan dubu 10.5 a cikin wa´adin shekaru 7. Sabon kasafin kudin kungiyar na euro miliyan dubu 862 da zai yi aiki har shekara ta 2013, ya hada da wani nazari da hukumar kungiyar EU zata yi akan dukkan kudaden da kungiyar ke kashewa ciki kuwa har da na fannin aikin noma kafin shekara ta 2009. Da farko dai tattaunawar ta cije a game da rangwamin da ake yiwa Birtaniya da tallafin da ake ba manoman Faransa da kuma bukatar da kasashen gabashin Turai membobin kungiyar suka gabatar na neman karin taimako raya kasa. SGJ Angela Merkel ta taka muhimmiyar rawa wajen cimma yarjejeniyar, inda ta ba da shawarar a karawa kasafin kudin euro miliyan dubu 13 don cike wani gibin da ka iya tasowa. Merkel ta bayyana yarjejeniyar da cewa wani kyakkyawan daidaito ne.