1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cimma yarjejeniya da gwamnatin Sudan

Nan da yan kwanaki kalilan ne ake saran isan jamian bada shawarwari na MDD guda 175,domin tallafawa dakarun kasashen Afrika wajen tabbatar da tsaro a lardin Darfur.Wannan na kunshe ne cikin wata samnarwar hadin gwiwa data fito daga ofisoshin Mdd da na KGA,dake kasar ta Sudan.Itama ma a nata bangaren,gwamnatin Khartum ta tabbatar da amanarta adangane da zuwan rukunin farko na kwararrun jamian MDD zuwa lardin Darfur.Yawancin kwararrun jamian dai sun fito ne daga kasashen Afrika da yankin Asia.