An cimma tudun dafawa a taron birnin Beijing | Siyasa | DW | 13.02.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An cimma tudun dafawa a taron birnin Beijing

Koriya Ta Arewa ta amince ta lalata tashosohin ta na nukiliya nan da kwanaki 60 masu zuwa.

Wakilan kasashe 6 a taron Beijing

Wakilan kasashe 6 a taron Beijing

Wannan dai shi ne kannun labaru a China da duniya baki daya. An cimma yarjejeniya bayan tattaunawa mai tsauri tsakanin wakilan kasashe 6, inda KTA ta amince ta yi watsi da shirinta na nukiliya, kamar yadda mataimakin ministan harkokin wajen China Wu Dawei ya nunar.

“Wannan sakamako na da muhimmanci ga zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci-gaban yankin tsibirin Koriya. Yana da muhimmanci domin kasashen yankin zasu iya inganta dangantaku tsakanin su. Muhimmi ne kuwa wajen wanzuwar kwanciyar hankali a gabashin Asiya.”

A cikin watanni biyu masu zuwa za´a fara aiwatar da matakin farko na rushe shirin nukiliyar KTA, inda kasar zata fara rufe manyan tashoshinta na nukiliya kana ta bari sofetoci na kashen waje shiga kasar. Bayan haka KTA ta nuna shirin ba da jerin tashoshinta na nukiliya.

Za´a fara saka mata da taimakon tan dubu 50 na danyen mai, sannan daga baya a ba ta taimakon makamashi da wasu tallafi, idan KTA ta rufe dukkan tashoshinta na nukiliya. An kuma yi alkawarin ba ta taimakon jin kai. Bugu da kari za´a duba bukatar KTA game da komawa kan teburin shawarwari tsakanin ta da Amirka. Kawo yanzu Amirka na adawa da yin wannan tattaunawa. A dangane da haka mataimakin ministan harkokin wajen China Wu Dawei cewa yayi.

“KTA da Amirka zasu koma ga tattaunawa tsakanin su da zumar yin musayawa yawu kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu. Hakan zai taimaka wajen karfafa dangantaku na kasa da kasa. Bugu da kari Amirka na da niyar soke sunan KTA a jerin kasashen da take zargi da marawa ta´addanci baya.”

Yarjejeniyar da ka kulla tsakanin kasashen 6 na matsayin wani canji na tarihi, bayan kai ruwa rana da aka dade ana yi tsakanin Amirka da KTA.

Tun kimanin shekaru 5 da suka gabata ake gudanar da shawarwarin na kasashe 6, inda ake kwan gaba kwan baya. Alal misali a shekara ta 2005 KTA ta amince ta lalata tashoshinta na nukiliya amma daga baya ta ki yin haka. Kawo yanzu ba´a taba samun wata matsaya kwakkwara dangane dakatar da shirin nukiliyar KTA kamar a wannan lokaci ba.

Yanzu haka dai an amince a koma zagaye na gaba na shawarwarin a Beijing cikin watan maris. Kafin wannan lokaci KTA zata dauki matakin farko na aiwatar da ka´idojin yarjejeniyar yayin da duniya kuma zata sa ido don ganin gwamnatin Pyongyang ta cika alkawarin da ta dauka.

 • Kwanan wata 13.02.2007
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtwE
 • Kwanan wata 13.02.2007
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtwE