An cimma sulhu a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango
December 31, 2016Talla
Rikicin siyasar dai ya samo asili ne bayan da shugaba Joseph Kabila ya ki sauka daga mulki a karshen wa'adinsa a ranar 20 ga wannan wata na Disamba da ke shirin kammala.Wani kakakin jami'an Cocin Roman Katolika na kasar da ke shiga tsakanin ya ce yau aka shirya za a baiyana sanarwa yarjejeniyar da za a rataba hannu a kanta.Kuma daya daga cikin abubuwan da yarjejeniyar ta tanada shi ne cewar joseph kabila zai ci gaba da yin mulki har zuwa sabuwar shekara ta 2017,lokacin da a aka shirya yin wani sabon zabe a kasar, sannan za a nada sabon firaminista da ya fito daga bangaran 'yan adawa.