An cimma arjejeniya tsakanin gwmnatin riko da kotunan islama na somalia | Labarai | DW | 23.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cimma arjejeniya tsakanin gwmnatin riko da kotunan islama na somalia

Gwamnatin rikon kwarya ta Somalia tare da wakilan kungiyar islama da ke rike da babban birnin kasar Mogadishu,sun rattaba hannu akan wata yarjejeniya wadda tayi kira ga gagauta tsagaita bude wuta tare da cewa kungiyar ta islama ta amince da halalcin gwamnatin wucin gadin,karkashin jagorancin shugaban kasar Sudan Omar al Bashir.

Sakatare janar na kungiyar kasashen larabawa Amr Musa ya fadawa manema labarai cewa,bangarorin biyu sun amince da dakatar da duk wasu tashe tashen hankula da ko farfaganda ta kafofin yada labarai domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar ta Somalia.

Amr moussa yace haka itama a nata bangare gwamnatin wucin gadin ta amince da kasancewar kungiyar ta islama.