An cimma ƙudurin faɗaɗa ayyukan Dakarun Jamus a Afganistan | Siyasa | DW | 26.02.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An cimma ƙudurin faɗaɗa ayyukan Dakarun Jamus a Afganistan

An tabka mahawara gabanin cimma matsaya dangane da faɗaɗa wa'adin Dakarun Jamus a Afganistan a majalisar dokoki ta Bundestag

default

Angela Merkel da Westerwelle

Majalisar dokokin tarayyar Jamus ta Bundestag, ta amince da kara yawan Dakarun ƙasar dake Afganista daga 4,500 na yanzu zuwa 5,350. An dai tabka zazzafar mahawara tsakanin wakilan majalisar kafin a cimma kara sojojin. 'Yan adawa  masu ra'ayin komunisanci dai sun soki  wannan manufa.

Mahawara dangane da manufofin Jamus a Afganistan ɗin dai bai yi nisa ba, aka ci karo da ɓarakar nan data ritsa da sojojinta a gundumar Kunduz . 'Yar majalisa Christiane Buchholz  daga jami'yyar adawa ta masu ra'ayin komusanci tana cikin masu adawa da wannan mataki..

" ko kuna so ko bakwa so, arangama da  waɗanda suka tsira da rayukansu ya tabbatar min da cewar, Jamus ta tsoma hannunta a yaƙi da talakawan Afganistan"

Bundesverteidigungsminister Karl-Theodor zu Guttenberg

Karl-Theodor zu Guttenberg

A daidai lokacin da ake kokarin cimma wannan manufa ta hanyar ku'riu a majalisar tarayyar Jamus din dai,  masu marawa  'yan majalisun dake da ra'ayin komusancin sun rike kwalaye dake ɗauke da sunayen waɗanda  hare-haren Boma-bomai na kunduz ya ritsa dasu a Afganistan.

Kimanin 'yan Afganistan 142 suka rasa rayukansu a watan Satumban bara, lokacin dakarun ƙungiyar tsaro ta NATO suka afkawa wata babbar tanki da aka sato da boma-bomai. Wani Kanar na sojin Jamus dake Afganistan ɗin ne dai ya bada umurnin wancan harin da aka kaiwa babbar mota ta sararin samaniya.

Da farko dai  shugaban majalisar Wakilan na Bundestag kuma ɗan jami'iyyar CDU mai mulki a Jamus Norbert Lammert ya umurci 'yan adawan dasu sauke kwalayen da suka ɗaga sama,da suka ki ya umurcesu dasu fice daga zauren majalisar..

" ina rokon ku da ku sauke waɗannan kwalayen,daga wannan lokaci na haramtawa dukkan wakilai da suka ki bin wannan umurni daga cigaba da kasancewa a cikin wannan zauren mahawara"

Bayan ficewar waɗannan 'yan majalisa daga zauren, kuma aka cigaba da mahawara, an ruwaito ɗan siyasa daga jami'iyyar adawa masu manufar kare muhalli Hans-Christian Ströbele yana cewa, koran wadannan 'yan majalisa  zai yi tasiri a ƙasar ta Afganistan, musamman a ɓangaren wadanda harin sojin Jamus din ya ritsa dasu....

Norbert Lammert im Sejm 20 Jahrestag Überwindung kommunistischer Diktaturen

Norbert Lammert

"Ban so haka ta kasance ba ko kadan. A ganina, hakan zai aike da mummunan sako zuwa Afganistan, da ma Duniya baki daya, domin zai nuna halayyarmu kan wadanda wannan yaƙin ya ritsa dasu, wanda kuma alhakin wuyanmu dama Jamus baki ɗaya ya rataya".

To sai dai shugaban Majalisar Lammert yayi tsayin daka kan matsayinsa dangane da 'yan adawan. Amma daga baya an bar 'yan adawn sun shiga majalisar domin kaɗa kuri'unsu adangane da faɗaɗa wa'adin dakarun Jamus ɗin a Afganistan.  'Yan majalisar 429 ne suka kaɗa kuri'un amincewa, ayayinda 111 sukayi adawa, kana wasu 46 suka ƙauracewa zaɓen.

Ministan harkokin waje Guido Westerwelle  dana tsaro na Jamus Karl Theodor zu Guttenberg  basu fito fili sun nuna goyon bayansu dangane da wannan manufa na gwamnatin tarayya ba. Sai dai majiya na nuna amincewar ɓangarorin gwamnatin haɗakar dangane da faɗaɗa wa'adin dakarun na Jamus a Afganistan.

Sai dai shugabar 'yan majalisar janmi'yar Greens dake kare muhalli, Renate Künast ta soki Westerwelle dacewar, maimakon ya shiga harkokin mahawara kan batutuwa na cikin gida yana ɓata sao'i 80 a makoka akan  tattauna  sabbin manufofin Dakaru Jamus a Afganistan. Shima shugaban SPD a majalisar kuma ya kasance ministan harkokin waje na wancan gwamnati yace babu alqibla a wannan lamari, duk kuwa da goyon bayan da suka bayar.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita : Ahmad Tijani Lawal