An cika shekaru da ƙaddamar da yaƙin Irak | Labarai | DW | 17.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cika shekaru da ƙaddamar da yaƙin Irak

A kwana a tashi, shekaru 4 kenan da sojojin Amurika su ka kiffar da tsohan shugaban ƙasar Irak, mirganyi Saddam Husain.

Albarkacin zaggayowar wannan rana, a ƙasashe daban-daban na dunia, an gudanar da zanga-zagar rashin amincewa da wannan yaƙi, da Amurika ta ƙaddamar a Irak.

Dubun dubunan jama´a, sun shirya zanga-zanga a biranen Washington, Samtambul, Copenhague, Madrid, Athenes, da dai sauran su, inda su ka yi ta rera kalamomin yin Allah wadai ,ga shugaban ƙasar Amurika Geoges Bush.

Saidai a wani mataki na ana magani kai na ƙaɓa, a yau ɗin nan ne opishin minsitan tsaro Amurika ya bayyana ƙarin tura dakaru a kasar Irak.

Daga farkon wannan yaƙi zuwa yanzu, a ƙalla sojojin Amurika 2.30 su ka sheƙa lahira, tare da dubun dubatar al´umomin Irak.