An cika shekaru 40 da ɓarkewar rikici a gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 05.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cika shekaru 40 da ɓarkewar rikici a gabas ta tsakiya

Kwana ta shi, yau shekaru 40 kenan daidai, da ɓarkewar rikicin da a ka raɗawa suna yaƙin kwnaki 6, a yankin gabas ta tsakiya.

A sakamakon wannan yaƙi Isra´ila ta mamaye wasu yankuna mallakar Palestinu, Syria da Jordan domin ƙara yawan fadin ƙasar.

Wannan yaƙi ya tsunduma gabas ta tsakiya baki ɗaya,cikin yanayin tashe-tashen hankulla, ba dare ba rana.

Albarkacin zagayyawar shekarun 40, Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia, Ban Ki Moon, ya gabatar da saƙon zaman lahia ga Isra´ila da Palestinu.

Ya gayyaci ɓangarorin 2, su dakatar da yaƙar juna, su kuma koma kann tebrin shawarri, wadda itace hanya ɗaya tilo ta cimma zaman lahia.

A nasa jawabi shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas,ya bayyana zullumin Palestinu, na fasɗawa cikin yaƙin bassasa a maimakon haɗa kai, domin tunkara ƙalubalen bani yahudu abokan gaba.