280910 Guinea Massaker Jahrestag
September 28, 2010Ƙungiyar Kare haƙƙin bil Adama ta Human Wrights Wacht ta bukaci hukumomi a ƙasar Guinea da su tabbatar da hukunci ta hanyar yiwa waɗanda a ka samu da laifin aikata kisan gilla a lokacin zanga zanga da aka gudanar a ƙasar a bara.
Sanarwa da Ƙungiyar ta bayyana, wacce ta zo a daidai lokacin da ake gudanar da zaman juyayin a yau na zagayawar cikon shekara guda da aikata kisan gillar da sojojin Musa Dadis Camara su ka aikata a ranar 28 ga watan Satumba na shekara ta 2009, akan jama´ar ƙasar ta Guinea na zaman ƙara jan hankali hukomomin.
Mutane a ƙalla 156, galibi ´yan adawa su ka rasa rayukansu a cikin zanga zangar.
Ibrahim Bary na ɗaya daga cikin waɗanda su ka tsira da rayukansu.
Ni ina ganin duk wanda ya aikata kisan gilla to ya kamata a hukunta shi, ya ce a lokacin zanga- zangar mun ga manyan sojoji da ministan tsaro su na bada umarni, amma kuma ya ce har yanzu ba a hukunta su ba.
Mawallafi: Abdourahman HassaneEdita: Yahouza Sadissou Madobi