An ci gaba da zanga-zangar matasa a daren jiya a kasar Faransa. | Labarai | DW | 09.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ci gaba da zanga-zangar matasa a daren jiya a kasar Faransa.

A dare na 13 a jere, matasa, mafi yawansu yaran makaurata baki da ke zaune a Faransa sun yi arangama da `yan sanda. Rahotannin baya-bayan nan da ke iso mana sun ce, wani gungun matasan, ya yi fito na fito da `yan sandan kwantad da tarzoma a birnin Toulouse, inda jami’an tsaron suka yi ta harba wa matasan barkonon tsohuwa, su kuma suna mai da martani da bam din fetur. A birnin Lyon kuma, wato birni na 2 mafi girma a Faransan, jami’an tsaro sun rufe duk tashoshin jiragen karkashin kasa, suka kuma dakatad da zirga-zirgan bas-bas da ke sufurin jama’a cikin birnin, bayan an jefa bam a wata tashar jiragen karkashin kasa. Har ila yau dai, mun sami rahotannin kone-konen motoci da wasu gine-ginen hukuma a birane da dama na kasar.

A halin da ake ciki kuma, wasu rahotannin na nuna cewa, rikicin Faransan dai na yaduwa zuwa wasu kasashen da ke makawbataka da ita. Farkon rahotannin da suka iso mana daga birnin Brussels na kasar Belgium sun ce matasa masu zanga-zanga sun kona motoci a babban birnin. Amma wata sanarwar `yan sanda ta ce rikicin bai kai irin na birnin Paris a Faransa muni ba.