An ceto daya daga cikin ′yan matan Chibok | Labarai | DW | 05.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ceto daya daga cikin 'yan matan Chibok

Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewar ta ceto karin wata yarinya daga cikin 'yan matan Chibok wadanda Kungiyar Boko Haram ta sace take kuma yin garkuwa da su sama da shekaru biyun da suka gabata.

Kakakin rundunar sojojin ta Najeriya kanar Sani Usman Kuka Sheka ya ce yarinyar mai suna Mariayama Ali Maiyanga wacce aka ceto a garin Pulka da a yankin Gwoza cikin  jihar Borno kan iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru,na dauke da yaro mai watanni goma wanda ta ce sunansa Ali.Ya zuwa an mika wannan yarinya ga cibiyoyin lafiya na sojoji don kula da lafiyarta.