An caji wasu da ayyukan ta´addanci a Biritaniya | Labarai | DW | 10.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An caji wasu da ayyukan ta´addanci a Biritaniya

Wata kotun kasar Biritaniya ta samu wasu mutane 4 da laifin dana bom din nan daya tashi a birnin London, a ranar 21 ga watan Juli shekara ta 2005. An dai caji mutane hudun ne da laifin hada baki domin gudanar da aikin kisan kai. An dai zargi mutanen biyu ne da laifin dana bom a hanyoyin sufuri na jiragen kasa a birnin na London, wanda hakan yayi ajalin mutane 52, da kuma jikkata wasu 700. Mutanen da ake zargi da wannan aikin dai sun shaidawa kotun cewa, bama baman su na bogi ne, kuma sunyi hakan ne don nuna adawar su da yakin da aka gabatar kann Iraqi.