1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cafke wasu mutane shida a Beljiyam

Masu bincike a kasar Beljiyam sun kama wasu mutane guda shida da ake zargi da hannu a harin da aka kai na ranar 22 ga wannan wata na Maris da muke ciki a birnin Brussels na kasar.

Belgien Brüssel nach Terroranschlag - Polizeieinsatz in Schaerbeek

Jami'an tsaro masu bincike a birnin Brussels na Beljiyam

Jami'an tsaron na Beljiyam dai sun aiwatar da binciken kwakwaf a wasu gidaje da ke karamar hukumar Schaerbeek a arewacin birnin Brussels da kuma Jette da ke yammaci, sannan kuma da tsakiyar birnin na Brussels a cewar wata sanarwa daga ofishin babban alkalin gwamnati. A wannan Alhamis din ne dai ministocin cikin gida na kasashen Turai suka yi zaman taronsu a birnin na Brussels inda suka yi fatan ganin an gaggauta cimma yarjejeniyar nan ta canjin muhimman bayanai da ma abin da ya shafi fasinjojin jiragen sama daga wannan kasa zuwa waccan a wani mataki na rigakafi wanda ya fi magani.