An cafke wani babban mai kishin islama a Indonesiya | Labarai | DW | 13.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cafke wani babban mai kishin islama a Indonesiya

Yan sanda a kasar Indonesia sunce sun kame wani babban mai kishin islama Abu Dujana wanda yake jagorantar wani bangare na kungiyar Jamaah Islamiya.

Ana dai zargin kungiyar ta jamaa Islamiya da laifin kai hari a Bali a 2002 da ma wasu hare hare da suka hada da harin da aka kaiwa ofishin jakadancin kasar Australia a birnnin Jakarta a 2004.

Yan sanda sunce sunyi anfani da kwajin kwayoyin halitta na DANN wajen gano Abu Dujana wanda yake anfani da lakani kusan guda shida.

Yan sandan sunce sun harbi Abu Dujana inda suka ji masa rauni cikin wani dauki da suka kai a tsakiyar lardin Java inda suka tsare wasu kuma bakwai tare da shi.