1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cafke mutane biyar kan harin Berlin

Zainab Mohammed Abubakar
March 29, 2018

Jami'an 'yan sanda a kasar Italiya, sun capke mutane biyar a bangaren binciken da ake yi kan harin ta'addanci da aka kai kasuwar Kirsimeti da ke birnin Berlin a 2016, wanda ake alakantawa da wani dan Tunisiya.

https://p.dw.com/p/2vCki
Deutschland Sicherheit auf Weihnachtsmärkten | Berlin ARCHIV
Hoto: Getty Images/AFP/C. Bilan

Anis Amri wanda Jamus ta hanawa izinin samun mafakar siyasa, ya afkawa kasuwar gargajiya kirsimeti a birnin Berlin da wata katuwar satacciyar mota, inda ya kashe mutane 12 tare da raunata wasu 100.

Mayakan IS sun dauki alhalin wannan harin na 19 ga watan Disamban 2016, wanda ke zama mafi munin harin da ya taba ritsawa da Jamus. Bayan kwanaki hudu da kai wannan harin ne 'yan sandan Italiyan suka harbe Amri a kusa da birnin Milan. 

Ana zargin mutane biyar da aka capke a yau Alhamis din da laifin ta'addancin kasa da kasa, daura da samarwa da 'yan cirani jabun takardu, a cewar kafofin yada labarun Italiyan.