An cafke matar tsohon gwaman jihar Delta ta Nigeria | Labarai | DW | 02.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cafke matar tsohon gwaman jihar Delta ta Nigeria

Yan sanda a Biritaniya sun cafke matar tsohon gwamnan jihar Delta wato Jemes Ibori. An cafke matar ne a filin jirgin saman Heathrow ne dake London, bisa zargin da akewa mijinta na safarar kudade ne izuwa ketare. Mr Jemes Ibori daya mulki jihar ta Delta har na tsawon shekaru takwas, a yanzu haka na fuskantar caji ne na safarar makudan kudade ne a wata kotu dake kasar ta Biritaniya.Tuni ma dai wannan kotu ta kwace kadarorin sa dake kasar, wadanda kudin su ya tasamma dalar Amurka miliyan 35.