An cafke maaikatan mai uku a nigeria | Labarai | DW | 11.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cafke maaikatan mai uku a nigeria

Maaikatan kamfanin mai na ketare guda uku ne aka sace a yankin Niger Delta dake kudancintarayyar Nigeria,a kusa da birnin Port Hacourt fadar jihar Rivers.

Kakakin kamfanin mai dake yankin Haz Iwendi,ya fadawa kamfanin dillancin labaru na AFP cewa daya daga cikin wadanda aka sacen ,dan kasar Italiya ne,a yayinda har yanzu baa tantance sauran jamiai biyun ba.Sai dai kakakin rundunar sojin dake yankin yace,sauran jamian biyu na iya kasancewa yan kasar India ne.Mr Iwendi yace a matsayinsu na jamian tsaro,suna kokarin ganin cewa an saki wadannan turawa uku da aka sace a yau,wanda yazo yini guda bayan bindige wani Ba Amurke dake aiki da kamfanin mai a birnin na Port hacourt.Rahotanni daga tarayyar Nigeriar dai na nuni dacewa,dukkan jamiai ukun da aka sace na aiki da kamfanin Saipem.