1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cafke Janar Léopold Mujyambéré

Abdourahamane HassaneMay 7, 2016

An kama Janar Léopold Mujyambéré jagoran Ƙungiyar 'yan tawaye ta FDLR na Rwanda. Ana zargin mutumin da hannu a kisan ƙare dangi da aka yi a Rwanda a shekara ta 1994.

https://p.dw.com/p/1Ijbt
DR Kongo Bevölkerung in Goma nach den Angriff der Hutu Rebellen
Wasu sojojin 'yan hutu a garin Goma na Jamhuriyyar Demokaraɗiyyar KwangoHoto: Getty Images/AFP/K. Maliro

Hukumomin a Jamhuriyar Demokaraɗiyyar Kwango sun ce sun kama wani ƙusa da ke da hannu a kisan ƙare dangin da aka yi a Rwanda a lokacin yaƙin basasar ƙasar a shekara a 1994 wanda a ciki aka kashe mutane dubu ɗari takwas galibi 'yan Tutsits da 'yan Hutus masu sassauci ra'ayi.

An kama Janar Léopold Mujyambéré jagoran Ƙungiyar 'yan tawaye ta FDLR na Rwanda a lokacin wani bincike da 'yan sanda suka saba yi a garin Goma da ke gabashin Kwangon.Yanzu haka dai an tasa ƙeyarsa zuwa birnin Kinshasa inda wata kotun soji za yanke hukuncin inda za a yi masa shari'a ko Kwango ko kuma Rwanda.