An cafke Janar Léopold Mujyambéré
May 7, 2016Talla
Hukumomin a Jamhuriyar Demokaraɗiyyar Kwango sun ce sun kama wani ƙusa da ke da hannu a kisan ƙare dangin da aka yi a Rwanda a lokacin yaƙin basasar ƙasar a shekara a 1994 wanda a ciki aka kashe mutane dubu ɗari takwas galibi 'yan Tutsits da 'yan Hutus masu sassauci ra'ayi.
An kama Janar Léopold Mujyambéré jagoran Ƙungiyar 'yan tawaye ta FDLR na Rwanda a lokacin wani bincike da 'yan sanda suka saba yi a garin Goma da ke gabashin Kwangon.Yanzu haka dai an tasa ƙeyarsa zuwa birnin Kinshasa inda wata kotun soji za yanke hukuncin inda za a yi masa shari'a ko Kwango ko kuma Rwanda.