1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bukaci kungiyyayar Eu ta ci gaba da tallafawa yankin Palasdinawa

February 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7B

Babban magatakardar kungiyyar kasashen larabawa, wato Amr Mussa ya bukaci kungiyyar gamayyar turai data ci gaba da bawa yankin Palasdinawa tallafi na raya kasa.

Mr Mussa wanda ya fadi hakan a babban ofishin na Eu dake Brussels a kasar Belgium, ya kara da cewa ire iren wannan tallafi ba suna zuwa aljihunan jami´an gwamnati bane , illa dai ana amfani dasu ne wajen inganta rayuwar mutanen yankin.

Rahotanni dai sun nunar da cewa, kungiyyar ta Eu ta tsinci kanta ne a cikin wani hali na tsaka mai wuya, bayan da kungiyyar Hamas, kungiyya da sukewa kallon ta yan ta´adda ce ta lashe zamen yan majalisun dokoki na yankin da aka gudanar.

Bukatar ci gaba da agazawa yankin na Palasdinawa dai yazo ne a dai dai lokacin da kungiyyar ta Hamas ke shirye shiryen fara tattaunawar kafa sabuwar gwamnatin hadaka da jamiyyar Fatah ta shugaba Mahmud Abbas

A dai ranar 27 ga watan nan da muke ciki ne ake sa ran ministocin kasashen kungiyyar 25 zasu gudanar da wani taro, don yanke hukunci kann wannan batu da kuma wasu batutuwa da suka shafi kungiyyar ta Hamas.