1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bukaci koriya ta arewa tayi watsi da aniyarta ta kera makamin nukiliya

November 17, 2005
https://p.dw.com/p/BvKf

Shugaba Bush na Amurka da takwaran sa na Koriya ta kudu sun bayyana rashin goyon bayan su game da kokarin da koriya ta arewa take na mallakar makaman nukiliya.

Shugabannin biyu dai sun bayyana hakan ne bayan wata ganawar ido da ido da suka yi a babban birnin kasar , wato Seoul.

Bugu da kari shugabannin biyu sun kuma yi fatan gudanar da wani taron koli a nan gaba don sasanta rikicin dake tsakanin koriya ta kudun da kuma ta arewa a hukumance.

Wannan dai yaki da kasashen biyu suka yi a shekara ta 1950 zuwa 1953, ya haifar da asarar rayuka masu yawan gaske a hannu daya kuma da kawo darewar yankin izuwa gida biyu.

Bisa wannan darewa izuwa gida biyu da yankunan suka yi a matsayin kasashe biyu, shugaba Bush ya bayyana fatan sa na ganin cewa kasashen sun dawo yadda suke ada a nan gaba, a matsayin kasa daya alumma daya.