An bukaci a sassauta wa kasar Katar | Labarai | DW | 15.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bukaci a sassauta wa kasar Katar

Sarkin Katar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya kai ziyarar a Jamus da Faransa inda shugabanin kasashen biyu suka yi kira na sulhunta sabanin da ke a tsakanin kasar da wasu kasashen Larabawa.

Wannan ziyarar ta kasance ta farko da Sarkin ke yi tun bayan da kasashen da ke makwabtaka da kasarsa suka mayar da ita saniyar ware bisa zarginta da goyon bayan ayyukan ta'addanci, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana damuwarta kan matakin yanke hulda da kasar ta Katar da kasashen  suka yi inda ta ce tana fatan ganin an shiga tattaunawa don kawo karshen wannan sabanin, a na shi bangaren Emmanuel Macron na Faransa ya ce yana fatan ganin an dage takunkuman da aka sanyawa Katar nan ba da jimawa ba. Shugabanin biyu sun fadi hakan ne a yayin ganawar da suka yi da sarkin a ziyarar da ya kai fadarsu a wannan juma'ar.

A watan Yunin da ya gabata ne kasashen Saudiya da Masar da Bahrain da kuma Daular Larabawa suk yanke hulda tare da rufe kan iyakokinsu da kasar ta Katar.