1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude taron yini 6 kan cutar AIDS a birnin Toronto

Mohammad Nasiru AwalAugust 14, 2006

Mahalarta taron na mayar da hankali wajen sabbin matakan rigakafin dakile yaduwar cutar.

https://p.dw.com/p/BvTO
Taron MDD kan AIDS
Taron MDD kan AIDSHoto: AP

Taken taron na AIDS na karo 16, shi ne “yanzu lokaci ya yi da za´a tashi tsayin daka don yakar cutar.” A halin da ake ciki dai ana iya cewa MDD da kungiyoyin ba da taimakon raya kasa sun dan samu ci-gaba wajen rarraba magungunan rage radadin cutar musamman a kasashe matalauta. To sai dai kwayoyin cutar na saurin yaduwa fiye da ci-gaban da ake samu wajen dakile su. Alkalluma sun nunar da cewa mutane kimanin miliyan 40 ne ke dauke da kwayoyin HIV mai haddasa cutar AIDS ko Sida a fadin duniya baki daya. Wata ´yar kasar Indonesia da ake kira Freyka, wadda aka gano kwayoyin HIV shekara guda gabanin a haife ta, ta ce ba´a samu wani canji na a zo a gani ba. Tun kimanin shekaru 5 da suka wuce wannan matar mai shekaru 24 da haihuwa ta kamu da cutar AIDS.

Freyka:

“Har yanzu ana nuna mana wariya a ko-ina. Alal misali a bara wani likitan hakori ya ki ya duba ni saboda ina dauke da cutar AIDS.”

Wayar da kan jama´a shi ne muhimmin abu idan ana batun cutar ta Aids, musamman idan ana son a kawad da irin wariyar da masu dauke da kwayoyin cutar ke fuskanta da kuma hana wasu kamuwa da cutar. A bara kadai mutane miliyan 4 ne suka kamu da kwayoyin HIV a duniya baki daya. A saboda haka shugaban kamfanin harhada na´urar komfuta ta Microsoft, wanda kuma ke jerin wadanda suka yi jawabin bude taron, Bill Gates ya ce da sakiya.

Bill Gates:

“Dole ne mu inganta matakan riga kafi muddin muna son mu rage yaduwar HIV. Ba zamu iya kula da dukkan wadanda ke dauke da cutar ba, idan ba mu samu gagarumin ci-gaba a matakan riga-kafin ba.”

Ba ya ga matsalolin da ake cin karo da su a matakan kandagarkin, mahalarta taron na AIDS zasu kuma yi musayar ra´ayoyi game da ci-gaban da aka samu a binciken kirkiro sabbin magunguna masu inganci na yaki da cutar. To amma ga kasashe masu tasowa har yanzu samun magungunan da ake da su yanzun wata babbar matsala ce.

Saboda haka shugaban shirin yaki da cutar AIDS na MDD Peter Piot ya ce samun nasarar yaki da AIDS a kasashe matalauta ya dogara ga yawan kudi da taimako da kasashe masu arziki zasu bayar.

Peter Piot:

“Kasashe masu arziki a duniya sun yi alkawarin ware kashi 0.7 cikin 100 na jimilar kudaden shigar su a shekara ga taimakon raya kasashe masu tasowa. Har in sun cika wannan alkawarin to za´a samu isasshen kudin da ake bukatar a yakin da ake yi da yaduwar AIDS.”

Piot ya ce shekaru 25 bayan bullar kwayoyin HIV yanzu lokaci yayi da za´a bullo da sabbin dubarun yaki da AIDS na dogon lokaci.

Ita ma Freyka daga kasar Indonesia ta ce yanzu lokaci na yin zallar fatar baka ya wuce. Ta ce dole ne a yi aiki zahiri a kuma cika alkawuran da aka dauka.

Ana sa rai taron wanda za´a kammala a ranar juma´a 18 ga wannan wata, zai samar da wani abin a zo a gani.