An bude taron sasanta tsakanin jama′ar Somalia | Labarai | DW | 19.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude taron sasanta tsakanin jama'ar Somalia

An bude taron sasanta tsakani na jamaar kasar somalia

Kafin bude taron anyi wani dan kwarya kwaryar yaki na mintuna talatin wanda ya birkita birnin Moagadishu na kasar Somalia yan saoi kadan kafin bude taron sasasnta tsakani a babban birnin kasar.

Rahotanni sunce mutane biyu aka kashe a cikin kasuwar Bakara a lokacinda dakarun gwamnati suka fafata da sojojin sa kai.

Wadanda suka ganewa idanunsu sunce yan bindigar sun kuma bude wuta kann ginin tsohuwar hedkwatar maaikatar tsaro inda yanzu haka yake a matsayin sansanin dakarun Habasha da suka taimaka korar mayakan islama daga birnin.

Taron na sasantawa a yau tun farko an shirya gudanarwa a ranar amma aka dage bayan wasu hare hare da aka kai kusa da gurin da aka shirya gudanar da taron.
Mayakan na islama sun lashi takobin hargitsa taron.