An bude taron kungiyar EU da shugabannin Latunamirka a Vienna | Labarai | DW | 12.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude taron kungiyar EU da shugabannin Latunamirka a Vienna

An fara wasu shawarwari masu muhimmanci tsakanin shugabannin kasashen KTT da takwarorinsu na Latunamirka a Vienna babban birnin Austria. A cikin wani daftarin sanarwar hadin guiwa da suka bayar shugabannin kasashen yankunan guda biyu sun yi kira da a kara nuna adalci a huldodin kasuwanci tsakanin kasashen kungiyar EU da na yankin Latunamirka. Wasu jami´an EU sun yi kashedi musamman ga kasashe kamar Bolivia da Venezuella game da matakan da suke dauka na yiwa kamfanonin hakan mai na ketare kora da hali daga kasashen biyu. Taron na kwanaki 3 dake samun halarcin shugabannin 60 zai kuma mayar da hankali akan hauhawar farashin man fetir a duniya da kuma batun kiyaye hakin bil Adama. Masu lura da al´amuran yau da kullum sun ce da wuya sassan biyu sun cimma wata yarjejeniya akan wani shirin hade huldodin cinikiyya, wanda ya dade yana hana ruwa gudu a tarukan baya.