An bude taron kolin kungiyar G-8 a St. Petersburg na Rasha | Labarai | DW | 15.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude taron kolin kungiyar G-8 a St. Petersburg na Rasha

Shugabannin kungiyar kasashe masu tagomashin tattalin arziki a duniya wato G-8 sun fara taron koli a birnin St. Peterburg na Rasha tare da cin abincin dare. Jami´an Rasha sun ce rikicin ake fama da shi a yankin GTT zai mamaye tattaunawar da shugabannin zasu yi. Hakan kuwa ya sa Rasha ta yi watsi da ajandar taron da farko wadda da zai fi mayar da hankali akan makamashi. Yanzu dai mahalarta taron zasu gudanar da shawarwari akan matakan soji da Isra´ila ke dauka kan Libanon da kuma Zirin Gaza. Shi ma taron kasashen Larabawa a birnin Alkahira da aka yi yau mayar da hankali ne akan wannan rikici.