An bude taron kolin kungiyar AU a birnin Banjul | Labarai | DW | 01.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude taron kolin kungiyar AU a birnin Banjul

Shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Afirka AU sun hallara a birnin Banjul na kasar Gambia inda zasu gudanar da taron koli. Muhimman batutuwan da za´a fi mayar da hankali a taron na yini biyu sun hada da halin da ake ciki a yankin Darfur mai fama da rikici a Sudan sai kuma halin da ake ciki a kasar Somalia. Manyan baki a taron kolin na birnin Banjul su ne shugaban Venezuella Hugo Chavez da shugaban Iran Mahmud Ahmedi Nijad. Masu lura da al´amuran yau da kullum sun ce halartar taron da Ahmedi Nijad zai yi wani yunkuri ne na neman goyon bayan kasashen Afirka a takaddamar da ake yi game da shirin nukiliyar kasar sa.