An bude taron kolin kungiyar ASEAN a karo na 12 a Filipins | Labarai | DW | 13.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude taron kolin kungiyar ASEAN a karo na 12 a Filipins

Shugabannin kasashen kudancin nahiyar Asiya sun fara taron kolin su na shekara shekara a tsibirin Ceto na kasar Filipins. An tsaurara matakan tsaro a taron na bana wanda shi ne karo na 12 a tarihin kafuwar kungiyar hada kan kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, shekaru 40 da suka wuce. Kungiyar mai membobi kasashe 10 ta amince ta sanya ranar da zata kafa wani yankin ciniki maras shinge kafin shekara ta 2015. An dage zaman taron a cikin watan desamba, bayan da kasashe dama ciki har da Amirka da Australiya da kuma Birtaniya suka yi gargadi game da yiwuwar kai wani hari a lokacin taron kolin.