An bude taron kolin kungiyar APEC a birnin Busan na Koriya Ta Kudu | Labarai | DW | 18.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude taron kolin kungiyar APEC a birnin Busan na Koriya Ta Kudu

An bude taron kolin shekara shekara na kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pacifik wato APEC a takaice a Busan birni na biyu mafi girma a KTK . Muhimmin batun da taron zai fi mayar da hankali a kai shine game da cimma yarjejeniyar cinikaiya sai batun yaki da masassarar tsuntsaye da kuma yaki da ayyukan ta´addanci na kasa da kasa. Taron dai ya hada shugabanni 21 na kasashe membobin kungiyar ta APEC ciki har da shugaban Amirka GWB da shugaban China Hu Jintao da FM Japan Junichiro Koizumi da shugaban Rasha Vladimir Putin da sauran masu fada a ji a fagen siyasar yankin. Dubun dubatan mutane sun gudanar da zanga-zanga a wurare da dama na birnin na Busan don nuna adawa da shugaba Bush.