1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude taron AU kan kasar Ivory Coast

October 17, 2006
https://p.dw.com/p/Bufb

AU/CONF

Shugabannin kasashen Afrika sun bude wani taronsu yau a birnin Addis Ababa na kasar Habasha don samo bakin zaren warware halin da kasar Ivory Coast take ciki.

Shugabannin kasashe 8 daga cikin kasashe 15 membobin majalisar tsaro ta kungiyar taraiyar Afrika da shuaga Laurent Gbagbo da kuma firaminista Charles Konan Banny suke halartar taron.

Ana sa ran zasu duba shawarar da shugabannin kasashen Afrika ta yamma karkashin ECOWAS suka bayar ba karawa shugaba Gbagbo karin sheakara guda bisa karagar mulki kafin zabe a kasar.

Hakazalika mahalarta ana sa ran zasu tattauna rawa da shugaban Afrika ta kudu Thabo Mbeki ke takawa na shiga tsakani a rikicin na Ivory Coast,kungiyar ECOWAS dai tana bukatar ya janye daga mai shiga tsakani saboda alaka na kut da kut daketsakanisa da Gbagbo.

Zaa mika sakamakon taron na AU ga komitin sulhu na majalisar dinkin duniya,wanda shi kuma zai tattauna akai ranar 25 ga oktoba