1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude taron AIDS a Majalisar Dinkin Duniya

Ministoci da kwararru na kiwon lafiya daga kasashe kimanin 200 sun hallara a birnin New York don gudanar da wani babban taron yini 3 akan cutar AIDS ko SIDA, da MDD ta kira. Ministar kiwon lafiya ta Jamus Ulla Schmidt zata wakilci kasar a wannan taro. Shekaru biyar bayan wani taron MDD na musamman, wannan taron zai duba irin ci-gaba ko akasin haka da aka samu akan matakan yaki da cutar ta kanjamau mai yin raga-raga da garkuwar jikin dan Adam. Yanzu haka dai gamaiyar kasa da kasa na fuskantar kalubale na rashin kudi a yaki da cutar a duniya baki daya. Alal misali a bara an bukaci dala miliyan dubu 15 amma miliyan dubu 8.3 kadai aka samu don yakar cutar ta AIDS.