An bude sake famfo a birnin Harbin na kasar China | Labarai | DW | 27.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude sake famfo a birnin Harbin na kasar China

Rahotanni daga China sun ce an sake bude ruwan fanfo a birnin Harbin wanda yayi fama da hadarin gubar Benzin. Kamar yadda kamfanin dillancin labarun kasar Xinhua ya rawaito, an bude famfo sa´o´i biyar gabanin lokacin da aka tsara da farko. To sai dai duk da haka hukumomi sun yi kira da a yi takatsantsan wajen shan ruwan famfo. Rahotanni sun ce yanzu haka dai ruwan kogin Songhua da ya gurbace da sinadarin Benzin, ya wuce birnin na Harbin. A tsakiyar makon jiya aka dauke ruwan famfo a birnin gabaki daya don kare mazauna daga gubar ta Benzin.