An bude ofishin Bankin Duniya na farko a Berlin | Siyasa | DW | 06.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An bude ofishin Bankin Duniya na farko a Berlin

Shugaban Bankin Duniya Zoellick da ministar raya kasashe ta Jamus Wieczorek-Zeul suka bude ofishin.

default

Wieczorek-Zeul da Zoellick

Ministar raya kasashen masu tasowa ta tarayyar Jamus Heidemarie Wieczorek-Zeul da sabon shugaban bankin duniya Robert Zoellick na masu ra´ayin cewa ana kan kyakkyawar turba a manufofin yaki da talauci a duniya baki daya. Ra´ayoyi na zuwa daya a batutuwa da dama na siyasa, inji ´yar siyasar ta jam´iyar SPD a lokacin bude ofishin bankin duniya na farko a Jamus, wanda aka kafa a hedkwatar hukumar ba da taimako da hadin kan fasaha wato GTZ a birnin Berlin.

An dace cewa dole ne a ci-gaba da mayar da hankali akan daukar nagartattun matakan yaki da talauci a nahiyar Afirka, inji Wieczorek-Zeul. To sai dai hakan ya dogara ne kan taimakawa tare da karfafa kula da kayayyaki mallakin jama´a, samar da kyakkyawan yanayi da ingantaccen tsarin kiwon lafiya da nuna adalci a huldodin cinikaiya da kuma kare muhalli.

1. O-Ton WZ:

“Mun amince mu ba da kudaden tallafawa wadannan matakan na gyara sannan a lokaci daya da ba da kudaden taimako don inganta hanyoyin samun sabbin dubarun makamashi ga kasashen masu tasowa. Hakan ya hada da taimakawa kasashen musamman na kurmi.”

Shi kuwa Robert Zoellick yayi tuni da ziyararsa ta farko a Berlin bayan nadin shi shugaban bankin duniya a dangane da alkawarin da kasashe masu arzikin masana´antu a duniya suka yi lokacin taron kolin su a Heiligendamm a farkon lokacin zafi na wannan shekara. Ya ce a lokacin kasashen da ake ba wa taimakon raya kasa sun nuna shakku ga alkawuran.

2. O-Ton Zoellick:

“Kasashen Afirka sun nuna fargabar cewa za´a karkata kudaden daga taimakon raya kasa zuwa fannin aikin sauyin yanayi. Daya daga cikin dalilan da ya sa aka ba da goyon baya kan soke wannan batu. Na biyu shi ne tsoron da kasashen suka nuna cewa zuba jari a batun kare muhalli ka iya rage bunkasar tattalin arzikin su. Amma ba na jin haka abun ya ke. Shi ya sa a taron da za´a yi kan yanayi a Bali, da ni da ministar raya kasashe masu tasowa ta Jamus da kuma kasar Indonesia wadda zata karbi bakoncin taron, zamu fadakar da cewa manufofin raya kasa da na sauyin yanayi dukka abu guda ne.”

A cikin watan disamba za´a gudanar da taron na Bali. Shugaban bankin duniya Roebrt Zoellick da ministar ta Jamus Wieczorek-Zeul sun yi kashedi da ka da a manta da kasashe kamar China da Indiya a batutuwan na kare muhalli. Suka ya ce ya kamata a taimakawa kasashen wajen samun wani ingantaccen tsarin kare muhalli musamman a dangane da karin makamashi da suke bukata saboda bunkasar tattalin arziki da suke samu.