1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude kan iyakar Gaza da Rafah

November 25, 2005
https://p.dw.com/p/BvJU

Shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas a yau ya kaddamar da bude kan iyakar Rafah dake tsakanin yankin zirin Gaza da kasar Masar kusan watanni uku bayan da rufe wannan kan iyaka kafin ficewar Israila daga yankin. Mahmoud Abbas ya baiyana bude kan iyakar da cewa za ta saukaka shige da fice domin sadar zumunci da yan uwan su dake kasar Masar. A yanzu dukkan Palasdinen dake da Pasfo, na iya wucewa kan iyakar ba tare da tsagwama ba. Jamián Palasdina sun baiyana fatan cewa bude kann iyakar zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin yankin.