An buɗe taron gwamnati da ƙungiyoyin islaman Jamus a Berlin | Siyasa | DW | 27.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An buɗe taron gwamnati da ƙungiyoyin islaman Jamus a Berlin

A yunƙuirn da gwamnatin tarayya ke yi na cim ma sajewar maƙaurata a cikin al'umman Jamus, ma'aikatar harkokin cikin gida ta taryya ta buɗe wani taro a birnin Berlin, inda aka gayyatao wakilai 15 daga ƙungiyoyin musulmi da kuma 15 daga karfofin tarayya da na jihohi da ƙananan hukumomi, don su yi tattauna batutuwan da ake ta ƙorafi a kansu game da addinin islaman a nan Jamus.

Ministan harkokin cikin gida na tarayya, Wolfgang Schäuble da takwaran aikinsa na jihar Baveriya, Günther Beckstein, a gun taron.

Ministan harkokin cikin gida na tarayya, Wolfgang Schäuble da takwaran aikinsa na jihar Baveriya, Günther Beckstein, a gun taron.

Taron dai ya kasance mai ma’ana, duk da cewa ba a sami jituwar duk mahalartan a kan wasu batutuwa ba. Bayanin da ministan harkokin cikin gida, Wolfgang Schäuble ya yi ke nan, bayan zaman da aka yi yau na buɗe farkon taron bita kan addinin islama a nan Jamus. Amma duk da haka, ya ce an yarje kan jigo ɗaya, wanda shi ne:-

„Addinin islama dai ya zaunu a nan ƙasar da ma Turai gaba ɗaya. Amma kuma, wajibi ne ga duk musulmin da ke zaune a Jamus da ma nahiyar Turai, da su mutunta ƙa’idoji da dokokin ƙasashen da suke zaune a cikinsu, don a tabbatad da samun zaman lumana tsakanin duk al’ummomi. A kan wannan batun dai, ba a yi wata jayayya ba, saboda babu ko mutum ɗaya da ya nuna adawa gare shi.“

Mahalarta taron dai sun ƙunshi wakilai 15 ne daga kafofin gwamnatin tarayya da kuma wakilai 15 daga zaɓaɓɓun ƙungiyoyin islama na Jamus. Sun kuma shafe awa uku suna tattaunawa a farkon zaman da suka yi yau. Jerin jigogin da za su tattauna a kansu dai na da yawa, kuma ana ganin cewa wakilai 15 na ƙungiyoyin islama ɗin, ba su isa su wakilci yawan musulmi kimanin miliyan uku da ke nan Jamus ba. Wato taron dai ba zai tattauna batutuwa tsakanin gwamnatin tarayya da musulmin Jamus kawai ba. Zai kuma dubi hulɗa ne tsakanin ƙungiyoyin musulmin da kansu. Akwai dai bambancin ra’ayi kan ko wace ƙungiya ce ta cancanci ta wakilci muslmin Jamus a taruka irin wannan, kuma ko wane ne zai yi magana da yawunsu ? Ministan harkokin cikin Wolfgang Schäuble, ya kuma ambaci wasu jigogin da ba a yarje a kansu ba tukuna:-

„An dai sami rashin jituwa a kan batun matsayin mata, musamman game da halayyar da ’yan matan musulmi za su dinga nunawa a makarantu. Ba dai abin mamaki ba ne da aka shiga cikin wannan halin.“

Su wakilan ƙungiyoyin islaman dai sun nuna gamsuwarsu ga yadda aka gudanar da taron na yau. Sun ce kowa ya sami damar faɗar albarkacin bakinsa ba tare da ya ji tsoron yin wani furuci ba. Badr Mohammed na ƙungiyar Turai ta faɗakad da kai da ke birnin Berlin ya bayyana cewa:-

„Akwai dai miliyoyinmu a cikin wannan al’ummar ta Jamus, to kamata kuwa yi mu bari a san da mu. A nan muke karatun firamare, da na sakandare har ma da karatun jami’a. Za mu dai yi farin cikin ganin cewa, a wannan taron bita kan addinin islama, mu ma sami dam ata bayyana kanmu a bainar jama’a.“

Wasu musulmin kuma na begen ganin cewa, addinin islama ma ya sami matsayin da hukuma ke bai wa coci-coci, tamkar wata kafa ta samo amfani ga jama’a. Kamar yadda Bekir Alboga na ƙungiyar islama ta Turkiyya a nan Jamus ya bayyanar:-

„Yau dai an fara wani shiri, inda muke fatar cewa, idan an kammala shi, hukuma za ta amince da addinin islaman tamkar wata kafar addini mai amfani ga jama’a mai kuma samun kariyar dokokin ƙasa.“

Wakilan hukumomin tarayya da na jihohi dai ba su ce uffan ba a kan waɗannan batutuwan, saboda ba sa son su yi wani jawabi cikin gaggawa a kan tattaunawar da za a shafe shekaru biyu zuwa uku ana yi. Za a kafa kwamitoci dai da za su yi muhawara kan batutuwan da aka fi ƙorafi a kansu, kamar manhajar koyad da addinin islama a makarantun gwamnati. A duk watanni 6 ne kuma za su gabatad da sakamakon da suka samu.

 • Kwanan wata 27.09.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btxz
 • Kwanan wata 27.09.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btxz