An buɗe taron ƙoli na Ƙungiyar Tarayyar Afirka a birnin Banjul. | Labarai | DW | 02.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An buɗe taron ƙoli na Ƙungiyar Tarayyar Afirka a birnin Banjul.

Taron ƙoli na Ƙungiyar Tarayyar Afirka, wanda aka buɗe jiya a birnin Banjul na ƙasar Gambiya, ya yi kira ga ɗaukan matakan gaggawa don warware rikice-rikicen da ake yi a ƙasar Somaliya da kuma yankin Darfur na ƙasar Sudan. Amma masharhanta na ganin cewa, babu alamun cim ma nasara a kan waɗannan batutuwan.

Jigon taron ne dai cim ma haɗin kan yankunan nahiyar, amma rikicin da ake ta fama da shi a yankunan arewa maso gabashin Afirkan, shi ne ya fi jan hankullan shugabannin ƙasashen da ke halartar taron. Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan, ya yi wa taron jawabi jiya, inda ya bayyana damuwarsa ga rikice-rikicen da ke ta aukuwa a nahiyar ta Afirka da kuma take hakkin ɗan Adam da ake yi a wasu kasashen nahiyar.