An buɗe taron ƙasa da ƙasa kan canje-canjen yanayi a birnin Bonn. | Labarai | DW | 15.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An buɗe taron ƙasa da ƙasa kan canje-canjen yanayi a birnin Bonn.

Yau ne aka buɗe taron ƙasa da ƙasa a nan birnin Bonn, don tattauna batun canje-canjen yanayi da ke ta ƙara janyo annoba iri-iri a yankuna daban-daban na duniya. Fiye da wakilai da jami’ai dubu, na gwamnatoci da kafofin ƙasashen duniya ne suka halarci taron, wanda za a shafe makwanni biyu ana yi, don tattauna yadda za a inganta matakan kare muhalli, bayan shekara ta 2012, yayin da wa’adin ɓangaren farko na yarjejeniyar na ta Kyoto zai cika.

Da yake jawabi a bikin buɗe taron, ministan muhalli na tarayyar Jamus, Sigmar Gabriel, ya ce sabon sakamakon da aka samu daga binciken baya-baya nan da masana kimiyya suka gudanar na nuna cewa, ɗumamar yanayi na ta ƙara haɓaka fiye da yadda aka yi hasashe a shekarun baya. Sabili da haka ne ya kamata duk ƙasashen duniya su ba da gudmmowarsu wajen tinkarar wannan ƙalubalen. Ministan ya ƙara da cewa, akwai bukatar shawo kan ƙasashe masu tasowa, musamman ma dai Sin da Indiya, don su ma su bai wa wannan fafutukar kare muhallin muhimmanci a tsarin manufofinsu. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

„Abin da ke da muhimmanci a nan shi ne, mu iya bayyana wa ƙasashe masu tasowan cewa, ba yunƙuri muke yi na angaza musu su amince da wani mizani na kare muhalli ba, wanda zai janyo cikas ga tattalin arzikinsu. A’a. Muna son mu nuna musu ne, yadda za su iya yin amfani da sabbin fasahohi na zamani, wajen bunƙasa tattalin arzikinsu, da inganta halin rayuwar jama’arsu, ba tare da gurɓata yanayi ba.“