An buɗe taro kan inganta tsaro a tekunan nahiyar Afirka a birnin Abuja. | Labarai | DW | 29.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An buɗe taro kan inganta tsaro a tekunan nahiyar Afirka a birnin Abuja.

Yau ne aka buɗe wani taron ƙasa da ƙasa na yini 3 a birnin Abuja na tarayyar Najeriya, don tattauna batun inganta tsaro da kuma shawo kan matsalar haɓakar ’yan fashi a kan tekunan nahiyar Afirka. Kusan wakilai ɗari 2 daga ƙasashe 47 da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa 13 ne ke halartar taron, inji Kyaftin Obiora Medani, na rundunar mayaƙan ruwan Najeriya, yayin da yake fira da kamfanin dillancin labaran AFP a birnin.

Taron, wanda Amirka ke ɗaukar nauyinsa, zai tattauna jigogi da dama ne, waɗanda suka ƙunshi harkokin tsaro a harabobin ruwan nahiyar Afirka, da hanyoyin tinkarar annoba, da gurɓacewar yanayi da kuma, inda ya cancanci a kafa cibiyar wata rundunar sojojin ƙundumbala na mayaƙan ruwa, masu shirin ko ta kwana, ƙarƙashin laimar Ƙungiyar Tarayyar Afirka, wato AU.

Game da batun tsaro a kan tekunan nahiyar dai, Kyaftin Medani, ya ce taron zai yi wani nazari mai zurfi ne kan wani rahoton da kwamandan rundunar mayaƙan ruwan Amirka a nahiyar Turai da Afirka, Admiral Harry Ulrich, ya gabatar. Ita dai Amirka, ta yi tayin ba da taimakon rundunar mayaƙan ruwanta don inganta tsaro a kan tekun Afirka Ta Yamma, inda take ganin ban da ’yan fashi, akwai kuma masu sumogan namun daji, da miyagun ƙwayoyi, da masu fatauci da bil’Adama.

A farkon wannan watan ne dai, rahotanni suka ce, wasu ’yan fashi sun afka wa wani jirgin ruwan jigilar man fetur na Rasha a gaɓar tekun ƙasar Gini , inda suka yi awon gaba da duk kuɗin da jirgin ke ɗauke da shi.