1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

An buɗe babban masallaci a Duisburg

Masallacin wanda shi ne mafi girma a Jamus na matsayin kyakkyawar alamar ingantuwar zamantakewa.

default

Sabon masallacin birnin Duisburg

A ranar lahadi da ta gabata aka yi bukin buɗe sabon masallaci a unguwar Marxloh dake birnin Duisburg. Wannan wurin bauta na Musulmai wanda shi ne mafi girma a nan Jamus an gina shi ne a wannan unguwa dake zama ɗaya daga cikin unguwannin talakawa a birnin. Tsarin ginin masallacin dai ya ƙayatar ƙwarai da gaske, musamman ganin yadda aka kammala aikin ginin ba tare da wata matsala ko wata adawa ta azo a gani daga mazauna wannan yanki ba. An kai wannan matsayi ne saboda gagarumin haɗin kai da aka samu tsakanin gamaiyar ta Musulmi da al´umar yankin waɗanda aka shigar da su a tsare-tsaren aikin masallacin. Tun da farko fari an yi shirya tarurruka iri daban daban inda aka duba koke-kokensu da sauran batutuwa da ke shige musu duhu game da addinin Musulunci. To shirin na yau dai zai kawo muku yadda ta kaya ne a bukin buɗe wannan masallaci a unguwar ta Marxloh dake birnin Duisburg.

A ƙarƙashin taken haɗuwar al´adu daban daban aka gudanar da bukin buɗe wannan masallaci na birnin Dusiburg wanda aka kwashe tsawon shekaru fiye da uku ana aikin gininsa. An bayyana wannan ci-gaba da aka samu a matsayin wata kyakkyawar alama ta ingantuwar zaman cuɗe-ni in cuɗe-ka da tuntunɓar juna tsakanin mabiya addinai da al´adu daban daban a wannan ƙasa. Elif Saat shugabar sashen Ilimi da tuntuɓar juna na ƙungiyar musulam Turkawa a Jamus wato DITIB ta yi nuni da muhimmancin wannan ci-gaba da aka samu.

“Kasancewar mu a nan yau don buɗe wannan masallacin wani ƙaramin abin al´ajabi ne a wannan unguwa ta Marxloh. Saboda haka muna addu´a Allah Maɗaukakin Sarki ya sanyama wannan abin al´ajabi albarkar.”

Wannan abin al´ajabin dai ya tabbata ne sakamakon basira da kyakkyawan tsarin da aka aiwatar, domin wakilan gamaiyar ta Musulman Duisburg sun koyi darasi daga kura-kurai da kai ruwa rana da ake fuskanta wajen aiwatar da aikin gina Masallatai a wasu wurare na Jamus. Domin kaucewa shiga irin wannan matsala gamaiyar ta shigar da mazauna da sauran maƙwabta cikin tsare tsaren tafiyar da aikin. Nikolas Schneider shugaban majami´ar Evangelika a yankin Rheinland ya yaba da wannan manufar ba da bayanai a fili da gamaiyar ta bi.

“Tun da farkon fari wannan gamaiya ta yi ta faɗakar da jama´a a faɗin wannan yanki game da manufar wannan aiki da ta sa gaba. Hakan shi ne dalilin da ya sa aikin gina masallacin ya ta fi salin-alim ba da wata adawa ba da aka saba nunawa a wasu biranen inda Musulmai ke son gina wuraren ibada.”

Ga ɗaukacin mazauna wannan unguwar ta Marxloh, waɗanda yawancinsu masu asali da ƙasashen waje ne, na ganin masallacin a matsayin wani dalili na ƙarfafa guiwa ko da ya ke ba za su yi salla a ciki ba. Ga yadda wasunsu suka bayyana ra´ayoyinsu.

“Tun ana cikin aikin ginin masallacin ya ba ni sha´awa matuƙa. Domin na san a lokutan bukukuwa za mu iya shiga ciki ko haɗuwa ko dai yin wasu ayyuka na gari. Dukkan a nan muke da zama, kuma dole ne mu rayu tare. Wannan kyakkyawan abu ne.”

Ita kuwa wannan matar cewa ta yi.

“Wannan na nuni da yadda al´adarmu ta ke. Akwai wuraren taruruka a ciki, inda Jamusawa za su iya zuwa don ganin yadda muke tafiyar da addininmu. Ina ganin wannan abu ne mai kyau.”

Shi kuwa wannan matashin ya tofa albarkacin bakinsa kamar haka.

“Gaskiya wannan abin ban sha´awa ne kuwa ya burge ni. Tsarin da aka yi masa yayi kyau. Mahaifiyata wadda memba ce a ƙungiyar mata ta majami´ar katholika ta sha zuwa nan wurin tana ganawa da da matan wannan gamaiyar inda su kan tattauna game da aikin. Shi ya sa ina jin wata rana zan yi ƙoƙari in shiga cikin ginin don in kashe kwarkwatar ido na.”

Dubun dubatan mutane Jamusawa da Turkawa suka hallara a gun bukin, bisa wannan dalilin ne aka buga taken ƙasashen biyu a gun bukin.

Mehmet Özay shugaban gamaiyar ta birnin Duisburg ya ce yanzu kam sun samu gindin zama a wannan ƙasa.

“Ko shakka babu mu dukkanmu mun zama ´yan Duisburg, mun zama ´yan jihar North Rhein Westfali kuma mun zama Jamusawa. Kasancewarmu a nan gida mu ke kuma muna son mu ci-gaba da zama a nan saboda haka muka gina wannan sabon masallacin”

Waɗannan kalaman na Özay tabbas haka ne domin da wannan masallacin kam yanzu an buɗe sabon babi na kyautatuwar zaman cuɗe-ni in cuɗe-ka. Duk wani ginin masallaci kamata yayi ya zama wani wuri dake wakiltar musulmai da yadda suke tafiyar da addininsu ba da wata rufa-rufa ba. Haka dai ginin wannan masallaci ya nunar inda tun daga sama har ƙasarsa an yi masa manyan tagogin gilashi don bawa mai wucewa damar ganin abubuwan dake wakana a ciki. Wato kenan wannan masallacin mafi girma a Jamus ya banbanta da sauran masallatai. Hakan ya tabbata ne sakamakon zurfin turtuɓar juna tare da warware wasu batutuwan masu ɗaure kai inji firimiyan jihar North Rhein Westafalia Jürgen Rüttgers wanda shi ma yake cikin mahalarta bukin.

“Ni da kai na na san da akwai wasu tambayoyi da ke da wuya a yi su a bainar jama´a. Amma ya zama wajibi mu yi tambaya ko mulkin demoƙuraɗiyya da dokokin addinin Musulunci sun dace da juna? Dole ne a ba mu amsar wannan tambaya.”

Firimiyan na wannan jiha ta North Rhein Westafalia ya ce bai kamata a nemi amsar wannan tambaya daga masu tsattsauran ra´ayin addini ba, Ko da yake ba su da faɗa a ji a birnin na Duisburg.

“Jama´a ya kamata kun san cewa ga mulkin demoƙuraɗiyya a nan ƙasar ba ruwanmu ga addininka ko kai Kirista ne ko Bayahude ko Musulmi. Muhimmin abu ga makomar wannan ƙasa shi ne abin da ya haɗa mu, wannan abu kuwa shi ne kundin tsarin mulkinmu wanda ya bawa kowa yion addinin da yake so ba da wata tsangwama.”

Ga dukkan musulmai ba ma na unguwar Marxloh ta Duisburg kaɗai ba, yanzu suna iya buga ƙirji da wannan sabon ginin masallacin. Dole kuma tuntuɓar juna da ake yi tsakanin addinai ta ci gajiyar wannan sabon ginin. Domin da yawa daga cikin waɗanda ba Musulmai ba za su nuna girmamawarsu ga wannan masallacin. Duk wanda ya yi wannan aiki ya cancanci yabo kuma dole a giramama shi. Wannan girmamawar za ta samar da sabon ruhi ga dangantaka tsakanin Musulmai da waɗanda ba Musulamai ba a Duisburg da ma yankin Ruhr baki ɗaya.

Sauti da bidiyo akan labarin