1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

An buɗe babban masallaci a Duisburg

Masallacin mafi girma a Jamus alama ce ta kyautatuwar zamantakewa tsakanin al´ummomi.

default

Jama´a a bukin buɗe masallacin Merkez a Duisburg

A jiya a birnin Duisburg dake yammacin nan Jamus aka yi bukin buɗe wani masallaci mafi girma a cikin ƙasar. Wannan ci-gaban da aka samu wata alama ce ta kyautatuwar zaman cuɗe-ni in cuɗe-ka tsakanin mabiya addinai daban daban a wannan ƙasa.

An dai yi wani bukin ba tare da wata matsala ba. Dalilin haka kuwa shi ne manufofin yin bayanai a fili na gamaiyar musulman unguwar Marxloh dake a birnin nan Duisburg. Gamaiyar al´umar musulman Turkawa a wannan yanki ta gayyaci wakilai kimanin 3500 na addinai daban daban a duniya baki ɗaya don halartar wannan buki. A ƙarshe kamar yadda ´yan sanda suka nunar baƙi 6000 ne suka halarci bukin buɗe wannan masallacin cikinsu har da Turkawa da Jamusawa daga yankin baki ɗaya. A jawabinsa firimiyan jihar North Rhein Westfalia Jürgen Rüttgers ya goyi da bayan gina masallatai a Jamus a fili amma ba a ɓoye ba. Sannan a lokaci ɗaya ya yi kira ga dukkan sassan da abin ya shafa da su ƙara himmatuwa a ƙoƙarin kyautata tsarin zamantakewa tsakani.

Ya ce: "Lalle mun gaza cimma manufar zaman cuɗe-ni in cuɗe-ka tsawon shekaru 40 idan mai shekaru 70 ko 75 a yanzu wanda ya shigo Jamus a matsayin ma´aikaci tun yana matashinsa kuma ya ba da gudunmawa wajen gina wannan ƙasa amma har yanzu bai iya harshen Jamusanci ba. Bai kamata a ce haka ya faru ba."

Tun bayan kafa harsashin masallacin gamaiyar Turkawan a unguwar Marxloh ta duƙufa wajen wayarwa da jama´a kai, inda ta yi ta shirya tarukan musayar ra´ayoyi da ƙara fahimtar juna tsakanin addinai. Saboda haka a bukin buɗe masallacin wakilan majami´o´i a faɗin ƙasar baki ɗaya sun hallara. Nikolaus Schneider shi ne shugaban majami´ar Evangelika a yankin Rheinland, ya yaba da manufar ba da bayanai a fili na gamaiyar.

Ya ce: "Tun da farkon fari wannan gamaiya ta yi ta faɗakar da jama´a a faɗin wannan yanki game da wannan aiki. Dalilin da ya sa ke nan aikin gina masallacin ya ta fi salin-alim ba da wata adawa ba saɓanin yadda muka shaida a wasu biranen."

Ɗaukacin Jamsusawa mazauna birnin na Duisburg sun amince da gina masallacin kamar wannan mutumin.

Ya ce: Shigar da dukkan maƙwabta cikin mahawwarar wannan aiki abu ne da ya dace. Idan muka haɗa kai muka yi aiki tare to za mu samu kyakkyawan sakamako a kullum."

Bukin buɗe masallacin a jiya shi ne farko a wannan makon inda a yau za a ci gaba da tarukan faɗakarwa da ƙarawa juna sani musamman game da samar da mahaja ta bai ɗaya ta koyar da darussan addinin muslunci a makarantun masu zaman kansu a Jamus. Daga cikin euro miliyan 7.5 da aka kashe wajen aikin jihar North Rhein Westfalia da tarayyar Turai sun ba da euro miliyan 3.2.