1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An buɗe gasar ƙungiyar Kwaman-Wealth

October 3, 2010

A ƙasar Indiya dubban mutane suka hallarci buɗe wasannin ƙasashen renon Ingila

https://p.dw.com/p/PTQo
Bukin buɗe wasannin CommonwealthHoto: picture alliance/dpa

An yi shagulgulan buɗe gasar Kwaman wealth a ƙasar Indiya, inda aƙalla mutane dubu sittin suka hallara. An tsaurara matakan tsaro, a wani matakin da gwamnatin ƙasar ke ɗauka don kaucewa abun kunya, biyo rahotanni da aka bayar gabanin buɗe gasar, inda aka ce birnin New Delhi bai shiryawa karɓar baƙin ba. An yi ƙiyasin jami'an tsaron na 'yan sanda da sojoji kimanin dubu ɗari ke aikin tabbatar da tsaron lafiyar 'yan wasa, da baƙi da ma wuraren guje-gujen. Buɗe gasar da aka yi ya samu hallartar shugaban ƙasar Indiya Parathiba Patil da Firai ministan ƙasar Manmohan Singh. Manyan baƙi sun haɗa da Yerima Charles na Ingila. A gobe ne dai za'a fara gasar.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammad Nasiru Awal